Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Bukaci Isra'ila Ta Janye Daga Yankunan Falasdinawa - 2002-04-05


Shugaba Bush yayi kira ga Isra'ila da ta janye daga yankunan Falasdinawan da ta shiga cikin 'yan kwanakin nan, amma jami'an Isra'ila sun sake jaddada cewa zasu ci gaba da kai farmaki har sai sun murkushe abinda suka kira ta'addanci.

A lokacin da yake magana jiya alhamis a fadar White House, Mr. Bush ya kuma yi kira ga shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, da yayi bakin kokarinsa domin kawo karshen ta'addanci.

Isra'ila da Falasdinawa duk sun yi marhabin da furucin shugaban na Amurka.

Jami'an Isra'ila sun ce sun goyi bayan kokarin Amurka na kawo karshen ta'addanci. Shugaban Falasdinawa Yasser Arafat, ya fada ta bakin wani kakakinsa, cewar yayi na'am da kokarin wanzar da zaman lafiyar na shugaba Bush ba tare da wata ka'ida ba, kuma yana rungume da shirin samar da zaman lafiya.

Har ila yau kuma, shugaba Bush ya ce a cikin mako mai zuwa zai tura sakataren harkokin wajensa, Colin Powell, zuwa yankin Gabas ta Tsakiya domin yayi kokarin ganin an cimma tsagaita wuta. Sai dai kuma, jami'an Falasdinawa sun ce wannan kokari na Amurka ba zai tsinana komai ba, idan har ba a samu sauyin abubuwan da suke faruwa ba a can a yanzu.

XS
SM
MD
LG