Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musharraf Ya Ce Zai Yi Amfani Da Makaman Nukiliya - 2002-04-08


Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya ce zai yi amfani da makaman nukiliya a kan kasar Indiya idan har ya zamo masa ala tilas.

A cikin hirar da yayi jiya lahadi da mujallar "Der Spiegel" ta kasar Jamus, Janar Musharraf ya ce idan har matsi yayi yawa kan kasar Pakistan, kuma ya zamo babu wani zabi, to zai juya kan bama-baman nukiliya kan babbar abokiyar gabar kasarsa.

Ya zargi Indiya da kokarin neman zamowa daya daga cikin hamshakan kasashen duniya, yana mai cewa ta dukufa ka'in da na'in wajen kerawa da tara makamai.

Kasashen biyu na Pakistan da Indiya sun shafe shekaru 55 suna rigima da junansu kan yankin nan na Kashmir.

A halin da ake ciki, babbar kawancen jam'iyyun siyasar Pakistan ta ce zata kauracewa kuri'ar raba-gardamar da za a yi cikin wata mai zuwa a kan ko Janar Musharraf zai ci gaba da zama kan karagar mulki na karin shekaru 5.

Kawancen Maido da Mulkin Dimokuradiyya, wadda ta kunshi jam'iyyu 15 ta ce wannan kuri'ar raba-gardama ta sabawa tsarin mulkin kasar.

A ranar Jumma'a Janar Musharraf ya bada sanarwar kuri'ar raba-gardamar, yana mai fadin cewa yana bukatar ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen siyasa tare da yaki da ta'addanci.

XS
SM
MD
LG