Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Bukaci Amurkawan Dake Gabas ta Tsakiya Da Suyi Taka Tsan-tsan... - 2002-04-11


Amurka ta bukaci Amurkawan ad suke yankin Gabas ta Tsakiya da su yi hattara sosai, koda za a sake ganin mummunar zanga-zangar nuna kin jinin Amurka kan farmakin sojan da Isra'ila take kaiwa a yankin Yammacin kogin Jordan.

Jiya laraba a kasar Bahrain, 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa da harsasan roba domin tarwatsa dubban masu zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa, wadanda ke yin Allah wadai tare da rera taken "Sai Mun ga bayan Amurka da Isra'ila" a kofar ofishin jakadancin Amurka da aka yi wa shinge mai yawan gaske a birnin Manama.

Har ila yau an gudanar da zanga-zanga a birnin al-Askandariyyu (Alexandria) a Misra, inda a ranar talata wani dalibi ya mutu a gwabzawar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa da 'yan sandan Misra.

XS
SM
MD
LG