Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 100 Ake Fargabar Sun Mutu A Tanzaniya - 2002-04-12


Gidan rediyon gwamnatin Tanzaniya ya ce ana fargabar mutane akalla 100 sun mutu, a bayan da jirgin ruwan kwale-kwale na jigilar fasinja da suke ciki ya nutse a wani kogin dake gabashin Tanzaniya.

Rahoton ya ce wannan hatsari ya faru jiya alhamis a kogin Kilombero.

Ba a san ko menene ya haddasa wannan hatsarin ba. Amma wani rahoto ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da igiyar da wani jirgin ruwa ke amfani da shi wajen janyo wannan kwale-kwale daga daya tsallaken kogin zuwa daya bakin gabar, ta yanke.

Jami'an 'yan sanda sun ce ya zuwa yanzu dai an gano gawarwaki 4. Akwai motoci guda hudu a cikin wannan kwale-kwale mai tsallakawa da mutane daga wannan gaba zuwa wancan a kogin.

XS
SM
MD
LG