Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kuskuren Matuki Ne Ya Haddasa Mummunan Hadarin Jirgin Saman China - 2002-04-16


Jami'an kula da zirga-zirgar jiragen sama na Koriya ta Kudu, sun ce watakila kuskuren matuki ne ya haddasa faduwar wani jirgin saman fasinja na kasar China, wanda ya kashe mutane akalla 119.

Jami'ai sun ce sun fadawa matukin wannan jirgi kirar Boeing 767-200 da ya sauya hanyar sauka jiya litinin a saboda iska mai karfin gaske dake zuwa ta goshin jirgin.

Hukumomi suka ce tana yiwuwa matukin, bisa tsautsayi, ya je ya ci karo da dutsen Shineo a lokacin da yake kewaya filin jirgin saman Kimhae a birnin Busan dake kudancin Koriya ta Kudu. An bada rahoton kasancewar iska mai karfi, da ruwan sama da kuma hazo mai yawa a lokacin da wannan jirgi ya fadi.

Mutane 39 daga cikin 166 dake cikin wannan jirgi sun kubuta da rayukansu. An ce daya daga cikin matuka jirgin yana daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu. An bada rahoton cewa ba a san inda mutane da dama suke ba.

An gano daya daga cikin na'urorin dake kula da abubuwan da suke faruwa a lokacin da jirgin ke tafiya.

XS
SM
MD
LG