Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Sarkin Afghanistan Zai Isa Birnin Kabul A Yau Alhamis... - 2002-04-18


Tsohon sarkin Afghanistan, Mohammed Zahir Shah, zai isa Kabul a yau alhamis, domin ziyararsa ta farko cikin shekaru kusan 30 a kasar tasa da yaki ya lalata.

Shugaban gwamnatin rikon kwarya, Hamid Karzai, yana rakiya ma sarkin daga kasar Italiya, inda ya koma da zaman hijira tun lokacin da aka tumbuke shi daga kan gadon sarauta a shekarar 1973.

Yau alhamis da asubahi mutanen biyu suka tashi daga birnin Rum tare da wasu ministoci 6 na gwamnatin Afghanistan. Mr. Karzai da 'yan Afghanistan da dama, da kuma jami'an kasashen duniya, suna fata tsohon sarkin mai shekaru 87 da haihuwa zai iya taimakawa wajen hada kan kabilun Afghanistan masu gaba da junansu.

An sha jinkirta tafiyarsa kasar a saboda damuwa kan tsaron lafiyarsa. Tsohon sarkin ya ce zai koma gida ne a zamansa na dan kasa, kuma ba ya da wani shiri na maido da gidan sarautar kasar kan karagar mulki.

XS
SM
MD
LG