Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Larabawa Sun Bukaci MDD Ta Binciki Mummunar Barnar Da Isra'ila Tayi A Jenin - 2002-04-19


Wakilan kasashen Larabawa a Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun bukaci a gudanar da binciken abubuwan da suka faru a sansanin ;yan gudun hijira na Jenin da aka yi wa mummunan ta'adi.

Kwamitin Sulhun MDD zai ci gaba da yin muhawara yau Jumma'a kan wani kudurin da zai umurci babban sakatare, Kofi Annan, ya gudanar da bincike. Jiya alhamis da maraice aka fara yin muhawara.

Har ila yau, kudurin yayi kira ga Isra'ila da ta janye daga yankunan Falasdinawa, ta kuma kawo karshen kofar-ragon da tayi wa majami'ar "Nativity" a Bethlehem da hedkwatar Malam Yasser Arafat a Ramallah.

Jami'ai suka ce watakila jakadan Amurka a MDD, John Negroponte, zai hau kan kujerar-na-ki, domin ya hana zartas da wannan kuduri.

A jiya alhamis, wani wakilin MDD na musamman dake rangadin ganin irin mummunar barnar da aka yi wa sansanin 'yan gudun hijira na Jenin, yayi Allah wadarai da kasar Bani Isra'ila a saboda ta hana kungiyoyin agaji shiga wuraren da suke bukata domin aikin ceto a cikin sansanin.

Wakilin na MDD, Terje (Terry) Larsen, ya ce babu abinda ke fita daga sansanin 'yan gudun hijira na Jenin im ban da warin mutuwa, kuma wurin kamar an yi girgizar kasa.An gwabza kazamin fada tsakanin Isra'ila da Falasdinawa a sansanin.

Mr. Larsen ya bayyana shawarar Isra'ila ta hana shiga sansanin a zaman "babban abin kyama ga zuciya", ya kuma bayyana halin da mutane ke ciki a wannan sansani a zaman "mai tsoratarwa fiye da duk yadda zuciya zata iya tunani."

Jami'an Falasdinawa sun yi zargin cewa kashe-kashen gilla kawai Isra'ila ta gudanar a sansanin, suna masu fadin cewa an kashe Falasdinawa fiye da 500. Isra'ila ta ce yawan wadanda ta kashe ab su kai haka ba.

XS
SM
MD
LG