Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Isra'ila Da Na Falasdinawa Zasu Sake Ganawa A Yau Laraba - 2002-04-24


Jami'an shawarwarin Isra'ila da na Falasdinawa suna nan suna shirye-shiryen sake yin taro yau laraba, domin tattaunawa da nufin kawo karshen kiki-kaka din da aka yi tsawon makonni uku a cocin nan na "Nativity" dake birnin Bethlehem.

Jami'an Falasdinawa sun ce koda yake jiya talata an yi ganawa mai ma'ana, amma kuma ba a kulla wata yarjejeniya ba. Yanzu haka dai, an yi kofar rago ga wasu mutane su dari biyu, ciki harda Falasdinawa 'yan bindiga a wannan coci dake yankin Yammacin kogin Jordan.

Da maraicen jiya talata ne, Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya shaida wa Isra'ila cewa, kada ta kuskura ta taba lafiyar shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, wanda ake ci gaba da killacewa a hedkwatarsa dake birnin Ramallah.

Wasu 'yan sa'o'i kafin wannan kashedi da MDD ta yi, sojojin Isra'ila suka fasa wata nakiya a cikin wannan hedkwata. Amma jami'an sojojin Isra'ila sun ce dakarun sun yi amfani da wasu nakiyoyi ne da ake takaita ta'adinsu, domin su lalata wasu makaman gurneti da aka tsinta a cikin wannan hedkwata ta Malam Arafat.

XS
SM
MD
LG