Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakin Basasa A Liberiya Yana Barazanar Tada Zaune Tsaye A Fadin Yankin - 2002-04-25


Wani rahoton da wata kungiyar bincike mai zaman kanta ta wallafa, ya ce yakin basasar da ake yi a cikin kasar Liberiya, yana barazanar yaduwa zuwa kasashen SAliyo da Gini makwabtanta, kana kungiyar tayi kira ga kasashen duniya da su tsoma hannu domin kawo karshen yakin.

Wannan rahoto da kungiyar ICG (International Crisis Group), mai hedkwata a birnin Brussels, ta bayar, ya ce samun zaman lafiya a cikin kasar Liberiya, shine sinadarin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin.

Kungiyar ta zargi shugaba Charles Taylor na Liberiya da laifin yin amfani da mayakan sa-kai 'yan kanzagi a kasashe makwabtansa. Kungiyar ta ce irin wannan matakin zai iya wargaza zaman lafiyar da aka sha wuya kafin a samu a kasar Saliyo.

Rahoton na kungiyar ICG ya yabawa kasashen duniya a saboda tsoma hannun da suka yi domin kawo karshen yaki a kasar Saliyo, yana mai kira gare su da su dauki irin wannan mataki a kasar Liberiya.

XS
SM
MD
LG