Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Ya Ce Ba Zai Gana Da Wakilan Isra'ila Ba... - 2002-04-25


A yau alhamis ake sa ran wakilan Isra'ila zasu bayyana a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya, MDD, domin su bayyana hujjojinsu na kin yarda da tawagar binciken da aka nada domin gano abubuwan ad suka faru a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun karkashe fararen hula masu yawa, abinda Isra'ilar ta ce ba haka ba ne.

Isra'ila tayi ikirarin cewa an kafa wannan tawaga ce da gangan domin a same ta da laifi. Tana son babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya kara kwararrun soja da na yaki da ta'addanci a cikin tawagar. Ta ce har ila yau, ya kamata tawagar ta binciki abinda ita Isra'ilar take cewa kungiyar 'yan ta'addar da ta karenta babu babbaka cikin sansanin na Jenin.

Amma kuma, kakakin babban sakataren, Fred Eckhard, ya ce Mr. Annan ba zai tattauna batun mutanen da ya nada a cikin wannan tawaga ba, haka kuma ba ma zai gana da wakilan na Isra'ila ba. Ya ce Isra'ila ta nuna zata yi aiki da duk wata tawagar da Mr. Annan ya nada, haka kuma babban sakataren yana ganin cewa shine yake da ikon nada jami'anta, ba wai wani ne zai fada masa ba.

Kakakin ya ce Mr. Annan yana sa ran tawagar zata isa Jenin ranar asabar. An jinkirta tashin tawagar domin bai wa wakilan na Isra'ila sukunin ganawa da wasu jami'an dabam an MDD a yau.

Falasdinawa suka ce wannan kumbiya-kumbiyar da Isra'ila take yi, alama ce dake nuna cewa akwai wani abinda take son boyewa. Isra'ila ta ce ba haka ba ne.

XS
SM
MD
LG