Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musharraf Ya Lashi Takobin Yada Sauye-Sauyen Dimokuradiyya - 2002-04-26


Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Pakistan, Pervez Musharraf, ya lashi takobin yada dimokuradiyya tare da yakar talauci idan har kuri'ar raba-gardamar da za a gudanar ranar talata ta nuna cewa masu jefa kuri'a suna son ya ci gaba da mulki na karin shekaru biyar.

Janar Musharraf ya kwace mulki a wani juyin mulkin da aka yi ba tare da zub da jini ba a shekarar 1999, sannan a shekarar da ta shige ya ayyana kansa a zaman shugaban kasa.

Janar Musharraf ya ce yana bukatar ci gaba da zama kan karagar mulki domin ya ci gaba da sauye-sauyen siyasa. Yayi alkawarin gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki nan da watan Oktoba.

Jami'an Pakistan sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuta cewa kasar tana yin marhabin da 'yan kallo na kasashen waje da su je su domin sanya idanu kan kuri'ar raba-gardamar ta mako mai zuwa.

XS
SM
MD
LG