Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Kwamitin Sulhun MDD Tana Rangadin Kasashe 8 A Afirka... - 2002-04-29


Wata tawagar Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta isa Pretoria, babban birnin Afirka ta Kudu, domin tayi kokarin karfafa yunkurin samar da zaman lafiya a Kwango Kinshasa da Burundi.

Wannan tawaga mai wakilai 15, zata ziyarci kasashe takwas: Afirka ta Kudu, Zimbabwe, Angola, Uganda, Tanzaniya, Burundi, Kwango Kinshasa da kuma Rwanda. Burin wannan tawaga shi ne karfafa takaitacciyar yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin biyu daga cikin sassa uku masu yakar juna a Kwango Kinshasa, a lokacin tattaunawar makonni da aka yi a Sun City, Afirka ta Kudu.

Tawagar ta MDD ta ce manufarta ita ce shawo kan sassan uku da su sake tattaunawa da junansu ta yadda za a iya cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin basasar kasar, wadda zata zamo karbabbiya ga dukkan sassan da abin ya shafa.

Har ila yau, tawagar ta MDD zata gana da bangarorin kasar Burundi, inda yakin basasa na tsawon shekaru 9 ya yi sanadin mutuwar mutane akalla dubu 200.

Tawagar zata gana da sassan an Burundi a kasar Afirka ta Kudu.

XS
SM
MD
LG