Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun MDD Ya Ce Yana Sa Ran Isra'ila Zata Hada Kai Da Tawagarsa - 2002-04-29


Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya ce yana sa ran jin "amsa ta kwarai" daga Isra'ila a kan ko zata bada hadin kai ga tawagar binciken majalisar da aka tura sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

Shugaban kwamitin mai ci, Sergei Lavrov an Rasha, shi ya bayyana wannan da maraicen lahadi, a bayan wani zaman gaggawa da kwamitin yayi domin muhawara kan kudurin da zai bukaci Isra'ila ta yi aiki da tawagar.

Ma'aikatan jakadanci suka ce babban sakataren majalisar, Kofi Annan, ya bukaci da a ba shi karin sa'o'i 24, ko kwana guda, domin yayi kokarin warware sabanin da aka samu.

A jiya lahadi, majalisar zartaswar Isra'ila ta jefa kuri'ar kin bada hadin kai ga wannan tawaga. Ministan sadarwar Isra'ila yayi kagen cewa MDD ta tashi haikan ne domin dora wa kasarsu "laifi ko ta halin kaka" a cewarsa.

Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun yi ta karkashe fararen hula cikin wannan sansani, yayin ad Isra'ila take cewa sun akshe Falasdinawa kimanin 50 ne a gwabzawa da 'yan bindiga.

XS
SM
MD
LG