Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rumbun Tara Makamai Yayi Bindiga A Kasar Guinea - 2002-05-06


Wuta da fashe-fashe masu yawa sun girgiza wani rumbun tara makamai jiya lahadi, a wani sansanin soja dake kusa da Conakry, babban birnin kasar Guinea.

Ba a samu wani rahoto nan take na mutuwa ba, amma wani soja dake sansanin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa irin barnar da wannan gobara da kuma fashe-fashe suka yi, tana da yawan gaske.

Kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ambaci jami'an hukumar kwana-kwana suna fadin cewa an samu nasarar shawo kan wutar.

Har yanzu kafofin yada labaran gwamnati ba su yi sharhi kan wannan lamari ba.

Mutane masu yawa sun mutu a cikin wannan sansani na soja, a lokacin da rumbun tara makamansa yayi bindiga watanni 15 da suka shige.

XS
SM
MD
LG