Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tsame Hannu daga Yarjejeniyar Kafa Kotun Aikata Laifuffuka Ta Duniya - 2002-05-07


Amurka ta shaidawa MDD a jiya litinin cewa ta tsame hannunta daga yarjejeniyar nan da ta kafa kotun duniya ta farko da zata ringa shari'ar aikata laifuffuka, a saboda za a iya yin amfani da ita wajen shigar da karar Amurkawa a saboda dalilai na siyasa a kasashen waje.

Wannan shawara tana nufin cewa Amurka ba zata amince da hurumin kotun ba, haka kuma ba zata yi aiki da umurninta ba.

Nan take kasashen duniya, cikinsu har da kawayen Amurka da dama, tare da Tarayyar Turai, suka fito suka yi tur da wannan shawara.

Ita ma kasar Canada, daya daga cikin kasashen da suka jagoranci kafa wannan kotu, ta bayyana jin takaicin wannan mataki da Amurka ta dauka, amma kuam ta ce wannan ba zai kaui ga mutuwar kotun ba.

Kungiyar Tarayyar Turai, wadda da ma take fushin yadda Amurka ta janye daga yarjejeniyar kare muhalli ta Kyoto, ita ma ta bayyana takaici.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Human Rights Watch" ta ce tarihi zai nuna cewa Amurka tayi kuskure da ta dauki wannan shawara.

Kasashe fiye da 60, cikinsu har da akasarin kawayen Amurka, sun rattaba hannun amincewa da yarjejeniyar kafa wannan kotu.

XS
SM
MD
LG