Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Sun Bukaci Matakan Sauye-Sauyen Siyasa - 2002-05-16


Shugabannin Falasdinawa sun ce suna son Yasser Arafat ya cika alkawarin da yayi na gudanar da sauye-sauyen siyasa, ta hanyar daukan kwararan matakai.

'Yar majalisar dokokin Falasdinawa, Hanan Ashrawi, ta ce al'ummar Falasdinawa suna bukatar tsarin lokacin gudanar da zabe. Wani babban jigo na kungiyar 'yan kishin Falasdinu ta Hamas, Isma'il Abu Shanab, ya ce kungiyarsa tana son sauye-sauyen zahiri, ta yadda za a kyale ra'ayoyi da bukatun kowa da kowa.

A cikin jawabin da yayi jiya laraba ga majalisar dokokin Falasdinawa, Yasser Arafat, yayi kiran da a sake nazarin dukkan mukamai na mulki ko na minista, tare da yin garambawul ga rundunar tsaron Falasdinawa. Ya bada shawarar da a yi shirye-shiryen gaggawa na gudanar da zabe, ya kuma ce har yanzu yana da kudurin cimma zaman lafiya da Isra'ila.

Fadar White House ta ce shugaba Bush ma yana son Malam Arafat ya dauki matakan yin sauye-sauyen da zasu kyautata rayuwar Falasdinawa tare da inganta yiwuwar cimma zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG