Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Mali Ta Ce Janar Toure Shine Shugaban Kasar Na Gaba - 2002-05-17


Gwamnatin Mali ta ce tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja, Amadou Toumani Toure, shine ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka yi ranar lahadi.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta bada sakamakon da ya nuna Janar Toure a kan gaba da kimanin kashi 64 daga cikin 100 na yawan kuri'un da aka jefa. Abokin takararsa, kuma dan jam'iyyar da take mulkin kasar a yanzu, Soumaila Cisse, ya samu kusan kashi 36 daga 100.

Rahotanni sun ce Malam Cisse ya kira Janar Toure ya taya shi murnar nasarar da ya samu.

Wannan sakamako zai zamo na tabbas da zarar kotun tsarin mulki ta kasar ta rattaba hannu kansa a mako mai zuwa.

Amurka ta yaba da zaben da aka gudanar a kasar Mali a zaman wanda aka yi "babu hauragiya, babu kuma ha'inci", tana mai nuni da cewa dukkan 'yan takarar sun amince da sakamakon zaben.

Mai maganada yawun ma'aikatar harkokin waje, Lynn Cassel, ta ce wannan zabe wani muhimmin mataki ne na kara karfafa mulkin dimokuradiyya a Mali.

Sabon shugaban da aka zaba zai maye gurbin shugaba Alpha Oumar konare, wanda a bisa tsarin mulki, babu damar ya nemi wannan kujera a karo na uku.

Janar Toure ya shiga cikin juyin mulkin 1991 wanda ya hambarar da gwamnatin shekaru 23 ta kama-karya ta Mousa Traore, ya kuma zama shugaban kasa na riko har zuwa lokacin da aka yi zabe a shekarar 1992.

XS
SM
MD
LG