Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Pakistan Sun Gano Gawar Da Ake Kyautata Zaton Ta Daniel Pearl Ce - 2002-05-17


'Yan sandan Pakistan sun ce sun yi imani da cewa sun gano gawar dan jarida Daniel Pearl na jaridar "Wall Street Journal" da aka akshe a kasar.

'Yan sanda suka ce wasu mutanen da aka tsare jiya alhamis, sune suka kai su wani wurin da mutanen suka ce an binne Mr. Pearl. Hukumomi suka ce an gano gawa a wurin, kuma ana yin gwaji domin tantance ko ta wanene.

Jami'an ma'aikatar harkokin wajen Amurka suna bayyana taka tsantsan wajen maida martani, a saboda rahotannin da aka yi ta samu a baya na samo gawar, amma kuma daga baya sai a gano cewa ba haka ne ba.

Sun ce suna sa ran zasu tuntubi hukumomin Pakistan a yau Jumma'a.

Mr. Pearl ya bace a cikin watan Janairu daga birnin Karachi mai tashar jiragen ruwa, inda yake kokarin rubuta wani labari a kan masu kishin addinin Islama.

XS
SM
MD
LG