Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Shugaban Kasar Saliyo - 2002-05-20


An sake rantsar da shugaban kasar Saliyo, Ahmed Tejan Kabbah, a wani sabon wa'adi na shekaru biyar, bayan da ya lashe fiye da kshi 70 cikin 100 na kuri'un da aka jefa a zaben ranar talata.

A wajen bukin rantsar da shi jiya lahadi, Mr. Kabbah yayi rokon da a samu hadin kan kasa. Har ilayau yayi alkawarin yakar zarmiya da yunwa tare da kare hakkin bil Adama a wannan kasar yankin Afirka ta yamma da ta shafe shekaru 10 tana fama da yakin basasa.

Ya ce al'ummar Saliyo sun yanke hukumci da kuma shawarwari mafiya muhimmanci a wannan zamani a tarihin kasar. Ya yaba da yadda aka gudanar da wannan zabe cikin lumana.

Duk da cewa 'yan adawa sun zargi hukumomin Saliyo da yin magudi tare da musugunawa a lokacin wannan zabe, 'yan kallo na kasashen waje sun ce wannan shine zaben da aka fi gudanar da shi cikin lumana tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga Ingila a 1961.

Magoya bayan jam'iyyar Mr. Kabbah ta "SLPP", wadda ta kuma lashe kujeru 83 cikin 112 na majalisar dokoki, sun fito suna kade-kade da rawa da wakoki domin murnar wannan nasara da suka samu.

Sakamakon zaben ya nuna cewa jam'iyyar da 'yan tawayen RUF, wadanda aka dora wa laifin gudanar da munanan ayyukan assha a lokacin yakin basasa, ba ta tsinana komai a lokacin wannan zaben ba.

Rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD mai sojoji dubu 17, ita ce ta taimaka wajen shiryawa ad gudanar da wannan zabe na Saliyo.

XS
SM
MD
LG