Shugaba Bush ya ce za a ci gaba da yin aiki da takunkumin cinikayyar da Amurka ta sanyawa kasar Cuba, har sai lokacin da shugaba Fidel Castro ya gudanar da zabe na Allah da Annabi, ya sako fursunonin siyasa, ya kuma yi gyara ga tsarin tattalin arzikin Cuba.
Mr. Bush yayi wannan furuci jiya litinin, a jawabin da yayi ga Amurkawa 'yan asalin Cuba a birnin Miami, wurin bukin cikar shekaru 100 da samun 'yancin kan kasar Cuba.
Mr. Bush ya bayyana shugaba Castro mai shekaru 70 da haihuwa a zaman mai kama karya, wanda ya kamata yayi sauye-sauye tun yana da lokaci a yanzu. Shugaba Bush ya ce Amurka ba ta son ci gaba da aiki har abada da takunkumi kan kasar Cuba, amma kuma ya ce tana son al'ummar Cuba su samu 'yancin walwala.
Tsohon shugaban Amurka, Jimmy Carter, yayi kiran da a dage wannan takunkumin a ziyarar da ya kai zuwa Cuba a makon da ya shige.
A halin da ake ciki kuwa, manyan 'yan adawar Cuba sun yi kira ga gwamnatin shugaba Bush da ta fara tattaunawa da Cuba.
Vladimiro Roca da Elizardo Sanchez sun saurari jawabin da shugaba Bush yayi jiya litinin kan Cuba daga can Havana. An ambaci Mr. Roca yana fadin cewa tattaunawar zata kawar da akasarin hujjojin shugaba Castro na ci gaba da yin amfani da tsarin siyasa mai jam'iyya daya tak.
Mr. Sanchez yayi marhabin da kalamun Mr. Bush kan kare hakkin bil Adama, amma kuma ya bayyana wasu kalamun shugaban na Amurka a zaman zancen kawai irin na zamanin zaman gabar akida.
A nan Washington, Sanata Chris Dodd dan jam'iyyar Democrat, ya ce shawarar da Mr. Bush ya yanke ta ci gaba da yin aiki da takunkumi a kan kasar Cuba, ta nuna cewa bai san irin muradun Amurkawa da majalisar dokoki ba.
Dan majalisar wakilai Henry Hyde dan jam'iyyar Republican kuwa, cewa yayi Mr. Bush ya gabatar da kwararan hujjoji, cewar rashin 'yancin siyasa da na tattalin arziki a Cuba ba su bada Amurka kwarin guiwar dage takunkumin ba.