Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Angola Ta Ce Amurka Da Wasu Kasashen Suna Tura Agajin Abinci Ga Tsoffin 'Yan Tawaye - 2002-05-22


Gwamnatin Angola ta ce Amurka da wasu kasashen sun fara aika abinci da kayayyakin agaji ga tsoffin 'yan tawayen UNITA, wadanda aka ce wasunsu suna mutuwa a sanadin rashin abinci mai gina jiki da kuma cututtuka.

An ajiye dubun dubatan 'yan tawaye a wasu sansanoni 38 da gwamnatin Angola ke gudanarwa, tun bayan shirin tsagaita wuta na watan jiya, wanda ya kawo karshen yakin basasar shekaru 27.

Jami'an Angola sun ce a jiya laraba ne jiragen sufurin kayayyaki guda biyu na Amurka suka isa Luanda, babban birnin kasar, dauke da tantuna da magunguna. Suka ce jiragen ruwa dauke da abinci ma sun fara isa daga wasu kasashen waje.

Kamfanin dillancin labaran AP ya ambaci wani kwamandan sojojin Angola, Janar Pedro Neto, ya ce tsoffin 'yan tawaye da iyalansu su kimanin 120 ne suke mutuwa a kowace rana cikin wadannan sansanoni a dalilin yunwa da cuta.

A ranar talata, babban mai bai wa MDD shawara kan kasar Angola, yayi kashedin cewa muddin ba a taimaka wa tsoffin 'yan tawayen cikin gaggawa ba, to zasu koma ga yin fashi, ko wani aikin na daba.

XS
SM
MD
LG