Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin MDD Sun Ce Miliyoyin Mutane Suna Cikin Kasada A Kasar Sudan - 2002-05-23


Hukumomin bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, suna gargadin cewa karancin abinci a yankin kudancin Sudan, zai shafi mutane akalla miliyan uku.

Hukumar Abinci ta Duniya ta ce kashi 30 daga cikin 100 kawai ya shiga hannunta, na kudidala miliyan 140 da take bukata domin samar da agajin abinci ga 'yan Sudan.

Asusun Tallafawa Yara na MDD kuma, UNICEF, ya ce shi ma ba ya da kudin ci gaba da gudanar da ayyukansa a kudancin Sudan.

Jami'in kula da ayyukan asusun UNICEF a kudancin Sudan, Sharad Sapra, ya ce babban abinda ke damunsu a yanzu shine abinda zai sami mutane miliyan daya a lardin yammacin Upper valley. Ya ce an yi wata da watanni da tsinke kudin gudanar da ayyuka a yankin.

Shi kuma darektan hukumar abinci ta MDD a Sudan, Masood Hyder, ya ce yayin da kungiyoyin agaji suke fargabar bala'in jinkai a lardin yammacin Upper Valley, an ga alamu masu kara kwarin guiwa a yankin tsaunukan Nuba.

Ya ce a jiya laraba aka fara jigilar abinci zuwa bangarorin gwamnati da na 'yan tawayen SPLA a yankin na Nuba, inda aka jima ana jan daga.

XS
SM
MD
LG