Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla Uku Sun Sheka Barzahu A Harin Kunar-Bakin-Wake A Isra'ila - 2002-05-23


Wani harin bam na kunar-bakin-wake da aka kai a garin Rishon Letzion na Isra'ila ya kashe mutane uku, cikinsu har da wanda ya kai harin.

Wasu mutanen su 20 sun ji rauni a wannan harin bam, wanda shine na biyu cikin wannan watan a garin dake kudu da birnin Tel Aviv. 'Yan Isra'ila 15 sun mutu a lokacin da wani Bafalasdine ya tada bam din da ya daura a jikinsa cikin wani dakin wasa a ranar 7 ga watan Mayu.

Wannan hari na jiya laraba, ya faru a wani wurin wucewar masu tafiya a kafa dake cike da mutane. 'Yan sanda suka ce wanda ya kai harin yayi kama da Ba-Ture, kuma ya rina gashinsa ya koma mai ruwan rawaya. Suna neman wata motar da aka gani ta sauki dan harin bam din kusa da wannan wuri, jim kadan kafin tashin bam din.

Rundunar Shuhada'u ta al-Aqsa, mai cibiya a cikin kungiyar al-Fatah ta Malam Yasser Arafat, ta dauki alhakin kai wannan harin.

Tun fari a jiya larabar, sojojin Isra'ila sun kashe wani jigon rundunar ta al-Aqsa kusa da birnin Nablus a Yammacin kogin Jordan. Majiyoyin Falasdinawa sun ce an kashe Mahmud Titi da wasu mutane biyu a lokacin da sojojin Isra'ila suka bude musu wuta a kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Balata.

A cikin wata sanarwa, kungiyar al-Aqsa ta ce zata kai karin hare-hare a kan 'yan Isra'ila.

Shugabannin Falasdinawa sun yi tur da harin bam din na Rishon Letzion, suna masu fadin cewa babu abinda zai haddasa im ban da bai wa Isra'ila hujjar kai farmaki da cin zarafin al'ummar Falasdinu.

XS
SM
MD
LG