Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Rokon Indiya Da Pakistan Da Su Kai Zuciya Nesa - 2002-05-23


Firayim minista Tony Blair na Britaniya ya roki Indiya da Pakistan da su tsaya su yi tunani sosai, kafin su dauki wani matakin da zai iya jefa yankinsu cikin fitina.

Mr. Blair ya shaidawa majalisar dokokin Britaniya cewa halin da ake ciki tsakanin kasashen biyu abokan gaba masu makaman nukiliya, yayi tsanani, kuma mai hadari ne ainun. Zai tura sakataren harkokin wajensa, Jack Straw, zuwa yankin a mako mai zuwa, domin kokarin warware zaman tankiyar.

Su ma jami'an Amurka suna rokon Indiya da Pakistan da su kai zuciya nesa, su rage tankiya ta hanyar tattaunawa. Sakataren tsaro, Donald Rumsfeld, ya ce yana tuntubar jami'an Indiya da na Pakistan. Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya tattauna halin da ake ciki ta wayar tarho da takwaransa na Britaniya, Mr. Straw.

A halin da ake ciki, a jiya laraba Indiya ta bukaci sojojinta da su shirya gwabza gagarumin yaki, yayin da Pakistan ta maida martani ta hanyar cewa abokiyar gabarta, zata same ta a shirye domin fuskantar irin wannan gumurzu.

Rundunar mayakan ruwan Indiya ma, ta tura wasu jiragen ruwan yaki guda biyar daga gabar gabashin kasar, zuwa cikin tekun Arabiya, kusa da Pakistan.

Tun da fari, shugaba Pervez Musharraf na Pakistan, ya ce yana son tattaunawa da Indiya, to amma kuma a shirye kasarsa take idan har Indiya ta kuskura ta kai mata hari. Har ila yau yayi watsi da zargin da Indiya tayi cewar Pakistan tana kyale Musulmi suna amfani da yankin kasarta wajen kai hare-haren ta'addanci kan yankin Kashmir na Indiya.

XS
SM
MD
LG