Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubun Dubatan Mutane Suna Fuskantar Bala'i Mai Tsanani Na Yunwa A Angola - 2002-05-27


Wata kungiyar agaji ta duniya ta ce yunwa tana yin barazana ga dubban mutane a lardin Huambo na kasar Angola.

Kungiyar nan mai suna "Doctors Without Borders" tayi kira ga gwamnatin Angola da kungiyoyin agaji na kasa da kasa da su kai abinci domin hana abkuwar abinda kungiyar ta kira kara tabarbarewar wannan lamari mai tsanani.

Kungiyar ta ce yawan yara kanana dake mutuwa da kuma bala'in rashin wadatar abinci a wasu sassan wannan lardi ya ninka na matsayin da za a iya cewa yayi muni sau biyar zuwa sau goma.

Har ila yau kungiyar ta bada rahoton dubban cututtuka masu alaka da rashin wadatar abinci a lardunan Huila da Bie.

Tun lokacin da aka cimma shirin tsagaita wuta a tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen UNITA a cikin watan Fabrairu, kungiyoyin agaji sun samu sumkunin kaiwa ga mutanen da fada ya sanya ba a iya kaiwa gare su a can baya.

XS
SM
MD
LG