Dan takarar indipenda a zaben shugaban kasa na Colombia, Alvaro Uribe, ya lashe zabe kai tsaye a bayan da ya samu fiye da rabin dukkan kuri'un da aka jefa.
Wannan ma shine karon farko da wani dan takarar shugaban kasa ya samu gagarumin rinjaye a zagayen farko an zabe a tarihin kasar.
Jami'an zabe suka ce Mr. Uribe ya lashe zaben na jiya lahadi da kimanin kashi 53 daga cikin 100. Wanda ya zo na biyu a zaben shine Horacio Serpa na jam'iyyar Liberal, wanda ya samu kimanin kashi 32 daga cikin 100.
Mr. Serpa dai ya yarda da cewa an kayar da shi.
Mr. Uribe yayi yakin neman zabe bisa alkawarin fadada rundunar sojojin kasar, tare da neman karin taimakon Amurka wajen murkushe 'yan tawaye amsu ra'ayin gurguzu.
A yanzu haka dai, Amurka tana bai wa Colombia agajin fiye da dala miliyan dubu 1 da 300, to amma an takaita yin amfani da wannan agaji ga aikin yaki da fataucin muggan kwayoyi kawai.
Tun fari, jakadiyar Amurka a Colombia, Anne Patterson, ta taya Mr. Uribe mai shekaru 49 murnar nasarar da ya samu, tana mai cewa Amurka zata ci gaba da yin hulda sosai da kasar Colombia.