Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nepal Ta Kara Tsawon Lokacin Yin Aiki Da Dokar-Ta-Baci - 2002-05-28


Sarki Gyanendra na kasar Nepal, ya sake kafa dokar-ta-baci na tsawon watanni uku, domin kokarin shawo kan tawayen masu akidar Mao (Tse Tung, tsohon shugaban kasar China) a wannan kasa dake yankin kudancin Asiya.

Dokar-ta-bacin ta bai wa jami'an tsaron ikon tsare magoya bayan 'yan tawayen masu akidar Mao, wadanda tun shekarar 1996 suke gwagwarmayar hambarar da gwamnatin mulukiyya ta Nepal domin su maye gurbinta da tsarin jam'iyya guda ta kwaminisanci.

Wannan matakin da aka fara daukar irinsa a watan Nuwamba domin shawo kan tawayen, an sake daukarsa bisa rokon gwamnatin Nepal da kuma firayim minista Sher Bahadur Deuba.

XS
SM
MD
LG