Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kumbon Amurka Ya Gano Kankara Karkashin Duniyar Mars... - 2002-05-28


Kumbon Odyssey na Hukumar Binciken Sararin Samaniyar Amurka mai kewaya duniyar Mars, ya gano wurare masu kankara da yawa a karkashin kasa dab da doron wannan duniya ta jar kasa.

An ambaci masana kimiyya a hukumar binciken sararin samaniyar ta Amurka suna fadin cewa gano kankarar zai iya gaggauta binciken ko akwai shaidar cewa an taba yin halitta a wannan duniya ta Mars.

Ana daukar ruwa a zaman abinda lallai sai akwai shi kafin a samu abkuwar halitta kamar yadda muka santa a nan duniyar Bil Adama. Ranar alhamis za a buga cikakken bayanin gano kankarar a mujallar kimiyya ta "Science."

A kwanakin baya ma, wannan kumbo dake kewaya duniyar ta Mars ya aiko da wasu hotunan da aka ga alamun cewa na koguna ne da suka kafe, da wuraren da aka yi ambaliyar ruwa, da kuma irin lakar nan da kan bazu idan an yi ambaliya, ko idan ruwa ya kafe.

A halin da ake ciki, wasu masana kimiyya na Ingila suna kera wani kumbo mai suna "Beagle 2 Mars Lander" wanda za a harba shi cikin babban kumbon "Mars Express" na hukumar binciken sararin Samaniya ta Turai a cikin watan Mayun 2003.

Kumbon na Beagle zai tona ya shiga karkashin duniyar ta Mars domin nemo ruwa, ma'adinai da alamu na halitta.

XS
SM
MD
LG