Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pentagon Tana Tsoron Cewa Pakistan Zata Janye Sojojinta Daga Bakin Iyakar Afghanistan - 2002-05-29


Jami'an tsaron Amurka sun ce suna fargabar cewa rikicin da ake yi a tsakanin Indiya da Pakistan yana iya gurgunta farautar da ake yi ta 'yan ta'addar kungiyar al-Qa'ida da dama wadanda aka yi amanna da cewa suna cikin lungunan yankin yammacin Pakistan.

Wata mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka ta ce akwai fargabar cewa Pakistan zata juya hankalin sojojinta kan Indiya, maimakon yin gadin bakin iyakarta ta yamma da Afghanistan domin hana mayakan al-Qa'ida sukunin sulalewa su koma cikin Afghanistan.

Kamfanin dillancin labaran AP ya ambaci wani babban jami'in ma'aikatar tsaron Amurka da ba a fadi sunansa ba, yana fadin cewa an ga alamun sojojin Pakistan suna shirye-shiryen tashi daga bakin iyakar.

A halin da ake ciki, kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan, Janar Franklin Hagenbeck, ya ce an yi imanin cewa shugabannin al-Qa'ida dake Pakistan suna kulle-kullen kai hare-hare a birnin Kabul domin gurgunta zaben sabuwar gwamnatin Afghanistan da za a yi a wata mai zuwa.

XS
SM
MD
LG