Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'in Amurka Ya Ce Duk Wani Agajin Da Za A Bada Kasashen Afirka Ba Zai Yi Tsinana Komai Ba... - 2002-05-30


Sakataren Bailtulmalin Amurka, Paul O'Neill, ya ce tura makudan kudaden agaji zuwa ga kasashen Afirka ba zai tsinana komai ba, sai fa idan an magance abubuwan da suke wakana a zahiri a nahiyar.

Mr. O'Neill, wanda yake rangadin kwanaki goma a Afirka tare da mawakin zamani dan kasar Ireland, Bono, yayi wannan furuci jiya laraba, lokacin da yake ganawa da 'yan jarida a Addis Ababa, babban birnin ethiopia, zangonsa na karshe a rangadin kasashe 4. Tun kafin nan, mutanen biyu sun ziyarci Ghana da Afirka ta Kudu da kuma Uganda.

Mr. O'Neill ya lura da cewa akwai alamun ci gaba, da na yiwuwar bunkasa sosai a Afirka, yayin da yake bayyana cewa a zahiri nahiyar tana bukatar karin agaji. Amma kuma ya ce tilas ne a mika kudin agaji ta hanyar da ta dace.

Tun da fari, Mr. O'Neill ya shaidawa wani taron Bankin Raya Kasashen Afirka a babban birnin na Ethiopia, cewar Amurka zata taimaka sosai, kuma ba tare ad kokwanto ba, wa dukkan kasashen Afirka da suka rungumi sauye-sauyen siyasa da na tattalin arziki.

Daya daga cikin dalilan wannan ziyara ta Mr. O'Neill ita ce nazarin hanya mafi nagarta, ta yin amfani da karin kudin agaji dala miliyan dubu 5 da gwamnatin shugaba Bush ta ware domin nahiyar Afirka.

A halin da ake ciki, mawaki Bono ya soki lamirin gwamnatin ta shugaba Bush, a saboda karin kudin rangwamen da ta bai wa manoman Amurka. Mr. Bono ya shaidawa 'yan jarida a Ethiopia cewar ba daidai ba ne ga Amurka ta hana wasu kasashen yin abinda ita kuma take yi gabanta-gadi.

XS
SM
MD
LG