Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilin Amurka Ya Kaddamar Da Sabon Yunkurin Samar Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya... - 2002-05-30


Wani babban wakilin Amurka yana yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da hukumomi a nan Washington suka kaddamar da sabon yunkurin gusawa da yankin ga cimma zaman lafiya.

mataimakin sakataren harkokin waje William Burns ya ce shugaba Bush yana da shirin samar da zaman lafiya mai matakai uku, wanda ya hada da komawa ga shawarwarin siyasa gadan-gadan da zai kai ga kafa kasashe biyu, watau kafa kasar Falasdinu wadda zata yi zaman lafiya da kasar Isra'ila makwabciyarta.

Har ila yau, ya ce Amurka zata taimakawa Falasdinawa wajen gina cibiyoyin gwamnati masu karfi da tasiri, tare da taimaka musu wajen hada kai da Isra'ila a fannin tabbatar da tsaro.

Mr. Burns yayi magana jiya laraba a birnin al-Qahira, a bayan da ya gana da ministan harkokin wajen Misra, Ahmed Maher.

A halin da ake ciki dai, Isra'ila tana nazarin irin martanin da zata maida ga hare-haren baya-bayan nan da Falasdinawa suka kai mata. A ranar talata, 'yan bindiga sun kashe 'yan Isra'ila hudu a yankin Yammacin kogin Jordan, yayin da su kuma sojojin Isra'ila suke ci gaba da kai farmakin soja a cikin yankunan Falasdinawa.

A wani labarin kuma, shugaban Falasdinawa Yasser Arafat, ya rattaba hannu kan dokar da zata zamo harsashin tsarin mulkin Falasdinu.

WAnnan doka ta fayyace irin ikon majalisar mulkin kai ta Falasdinawa da kuma majalisar dokokin Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG