Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Masu Gaba Da Juna A Madagascar Sun Dirkaki Juna A Wani Gari Na Arewacin Kasar - 2002-06-04


A bayan da aka wuni ana gwabza kazamin fada a Madagascar, sojoji masu biyayya ga mutumin da ya jima yana shugabancin kasar, Didier Ratsiraka, sun kasa sake kwato wani gari daga hannun sojojin abokin adawarsa, wadanda suka damke garin a karshen mako.

Sojoji masu goyon bayan sabon shugaban da aka rantsar, Marc Ravalomanana, sun ci gaba da rike wannan gari mai suna Sambava a arewacin kasar, a jiya litinin.

Kafofin labarai sun bada rahotannin cewa fada ya lafa a bayan faduwar rana, kuma a bayan mutuwar fararen hula biyu da soja guda.

KOda yake garin na Sambava yana da magoya bayan Mr. Ravalomanana da yawa, gwamnan wannan yanki mai goyon bayan Mr. Ratsiraka ne. Wannan gari an Sambava, shine cibiyar yankin nan dake samar da 'ya'yan itacen Vanilla masu matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasar.

Kama garin Sambava da sojoji masu biyayya ga Mr. Ravalomanana suka yi a karshen mako, shine farmakin farko da magoya bayansa suka samu nasarar kaiwa. Babban birnin kasar, Antananarivo, shi ma yana hannun magoya bayansa.

A ranar Jumma'a, dakarun Mr. Ravalomanana sun kasa kwace filin jirgin sama na biyu wajen girma a Madagascar, wanda ke birnin Mahajanga mai tashar jiragen ruwa.

Kasar Madagascar ta dare gida biyu a tsakanin magoya bayan abokan adawar tun lokacin zaben shugaban kasar watan Disamba da ake tabka rikici kai. A watan da ya shige aka rantsar da Mr. Ravalomanana a zaman shugaban kasa, a bayan da kotun kolin kasar ta yanke hukumcin cewa shi ya lashe zaben. Mr. Ratsiraka ya ki yarda da hukumcin kotun.

XS
SM
MD
LG