Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Zata Yi Kokarin Ganin An Ci Gaba Da Damawa Da Ita A Karawar Da Zata Yi Da Sweden - 2002-06-07


A yau Jumma'a ake shirin yin karon batta tsakanin Nijeriya da Sweden, yayin da Ingila zata gwabza da Ajantina, ita kuma Spain zata yi kokarin daukar fansa kan 'yan wasan Paraguay, duka a ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafar duniya.

Wasan farko zai gudana nan bada jimawa ba a birnin Kobe a kasar Japan, inda "Super Eagles" na Nijeriya zasu kara da 'yan Sweden.

Idan Sweden tayi nasara, to Nijeriya ba zata tsallaka zuwa zagaye na biyu ba, kuma hakan zai sa ita ma Ingila zata fuskanci barazanar jan burki a zagayen farko. A wasan farko, Ingila da Sweden sun yi kunnen doki da ci 1-1.

A wasa na biyu kuma, Spain zata yi kokarin daukar fansa kan Paraguay idan sun kara a Chonju, a kasar Koriya ta Kudu. A gasar cin kofin duniya ta baya, Paraguay tayi kunnen doki da 'yan wasan Spain, abinda ya sa suka wuce zagaye na biyu, ita kuwa Spain aka yi waje-rod da ita.

A garin Sapporo dake Japan, an ce za a dauki matakan tsaro sosai idan an zo karawa tsakanin manyan abokan adawa, Ingila da Ajantina, a wasan karshe na yau Jumma'a. Masu shirya wasannin suna fatan za a kaucewa irin abinda ya faru a Faransa a 1998, lokacin da 'yan kallo na kasar Ingila suka birkice, suka tayar da yamutsi a filin wasa.

XS
SM
MD
LG