Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce nan bada jimawa ba shugaba Bush zai bada sanarwar matakan samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da ra'ayoyinsa kan bunkasa tsaron kasar Isra'ila tare da kafa kasar Falasdinu.
Mr. Powell bai bayyana lokacin da za a bada wannan sanarwa ba.
Amma kuma ya ce nan bada jimawa ba wannan sanarwa zata fito, a bayan shugaba Bush ya tattauna cikin wannan mako da ministan harkokin wajen kasar Sa'udiyya, Yarima Sa'ud al-Faisal.
Wannan ziyara ta ministan harkokin wajen Sa'udiyya, ita ce zata kammala tuntubar musanyar ra'ayoyin fiye da watanni biyu da Amurka tayi da shugabannin yankin Gabas ta Tsakiya.
A cikin 'yan kwanakin da suka shige, Mr. Bush ya gana da firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila, da shugaba Hosni Mubarak na Misra.