Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senegal Ta Casa 'Yan Kasar Sweden A Fagen Tamaula - 2002-06-17


Yayin da Amurka da Mexico suke shirin kece raini yau litinin da sanyin safiya, tun jiya masoya kwallon kafa a kasar Senegal da ma fadin Afirka baki daya, suke ta tsalle da murnar doke 'yan wasan kasar Sweden da 'yan Senegal suka yi a ci gaba da gasar neman cin kofin kwallon kafar duniya.

Senegal dai ita ce kasar Afirka kwaya daya tak da ta rage a cikin wannan wasa a yanzu haka, kuma ita ce ta biyu a tarihin nahiyar, da ta taba kaiwa ga wasan kwata-fainal, a bayan da Kamaru ta taba yin haka a 1990.

Kafin a kai ga wasan na jiya, inda Senegal ta doke Sweden da ci 2 da 1, mai koyar da 'yan wasan Senegal, Bruno Metsu, ya ce 'yan wasan nasa, suna son bude wani sabon babi a tarihin kwallon kafar Afirka. Ko ba komai, 'yan wasan na Senegal sun rubuta wani sabon babi, cikin littafin nasarorinsu a wannan gasar cin kofin kwallon duniya na farko da suka taba halarta.

Gwarzo a cikin 'yan wasan Senegal a jiya dai, shine Henri Camara, wanda a cikin minti na 37 da fara wasa, ya ramo wa Senegal cin da 'yan Sweden suka yi tun cikin minti na 11 da fara wasa. Dadin dadawa kuma, shine ya jefa kwallon da ya bai wa 'yan Senegal nasara a cikin minti na 14 na karin lokacin da aka yi musu, bayan da aka tashi canjaras.

A bayan da aka yi karin lokaci, Sweden ta yi ta kai kora, kamar zata lashe wannan wasa, har ma wani dan wasanta mai suna Anders Svensson ya daki kwallon da ya bugi karfen ragar gola, ya kauce. Jim kadan a bayan wannan ne sai dan wasan Senegal mai suna Pape Thiaw ya daki kwallo da dunduniyar kafarsa zuwa ga Camara, wanda shi kuma bai bata lokacin cilla ta cikin raga ba.

A bayan wasan, mai koyar da 'yan wasan Senegal, Bruno Metsu, yayi magana da harshen Faransanci, inda ta bakin wani tafinta, ya yabawa 'yan wasan Sweden wadanda suka jima ba a doke su a fagen tamaula ba, yana mai cewa...

ACT: METSU INTERPRETER: "Mr. Metsu is really very, very happy happy..........."

FASSARA: tafintar ya ce kwach din Senegal, Mr. Metsu yana farin ciki sosai da ganin cewar 'yan wasansa sun doke wannan kungiya mai karfi ta kasar Sweden. Ya ce sau 16 a jere 'yan Sweden suna buga kwallo ba tare da an doke su ba. Ya ce a wasa na 17, Senegal tana farin cikin cewar ita ce ta doke 'yan Sweden din. A saboda haka Kwach Metsu yana farin ciki sosai.

Daga can Afirka kuwa, musamman ma a Senegal, ko ta ina ka duba jama'a murna suke yi da wannan nasara. A yanzu, Senegal tayi abinda 'yan wasan "Indomitable Lions" na Kamaru suka yi a shekarar 1990, watau sun je ga wasan kwata fainal.

A yanzu Senegal zata jira kasar da zata yi nasara a wasan da za a buga gobe talata tsakanin Japan da Turkiyya a garin Miyagi. Senegal zata kara da wadda tayi nasara ranar 22 ga watan nan na Yuni a birnin Osaka.

A yau litinin kuma, a ci gaba da wasannin zagaye na biyu na cin kofin kwallon kafar duniya, Amurka zata gwabza da makwabciyarta Mexico, yayin da Brazil zata yi kokari ta ga ko zata iya lallasa Belgium.

XS
SM
MD
LG