Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Tanzaniya Sun Dakatar Da Dukkan Ayyukan Hakar Ma'adinai - 2002-06-23


Hukumomin Tanzaniya sun dakatar da dukkan ayyukan hakar ma'adinai a gundumar Mererani na arewacin kasar, har sai masu aikin agaji sun tono gawarwakin ma'aikata masu hakar dutsen "Tanzanite" su akalla 42 da suka mutu a hadarin da aka yi ranar alhamis.

Jami'an gundumar sun ce ma'aikatan agajin sun fito da gawarwakin mutane akalla 11 zuwa doron kasa. Wannan hadari ya faru a lokacin da wani injin dake tura iskar shaka mai kyau zuwa cikin ramin hako dutsen, ya mace. Jami'ai suka ce akasarin gawarwakin suna wuri mai zurfin akalla mita 125 a karkashin kasa.

Wannan hadari shine mafi muni da aka yi a wani ramin hakar ma'adinai a kasar Tanzaniya cikin shekaru hudu. A shekarar 1998, ma'aikatan hakar ma'adinai akalla 70 sun mutu a gundumar ta Mererani, a lokacin da ruwan sama da aka tabka kamar da bakin kwarya yayi ambaliya ya toshe su cikin ramukan hako ma'adinai.

XS
SM
MD
LG