Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 500 Suka Mutu A Girgizar Kasa A Iran - 2002-06-23


Mutane akalla 500 sun mutu, wasu fiye da dubu 1 da 500 suka ji rauni a bayan wata girgizar kasa mai karfin gaske a arewacin Iran.

Jirage masu saukar ungulu da kungiyoyin agaji sun fara nemo wadanda ke da rai, sa'o'i a bayan wannan girgizar kasa ta jiya asabar, wadda ta kai awu 6 da digo 3 a ma'aunin motsin kasa na Richter. Cibiyar wannan girgizar kasa tana wani wuri mai tazarar kilomita 225 a yamma da birnin Teheran. Jami'ai suka ce suna tsammanin yawan mutanen da suka mutu zai karu, a saboda har yanzu akwai mutanen da gine-gine suka fada kansu suka rufe su.

Kamfanin dillancin labaran Iran, ya ambaci jami'ai a lardin Qazvin suna fadin cewa girgizar ta shafe kauyuka da dama daga doron kasa. Jami'ai suka ce gidajen laka na lardin suna rushewa da sauri a duk lokacin girgizar kasa. Dubban mutane sun rasa matsuguni a yanzu haka.

Wannan girgizar kasa da kuma kananan da aka yi ta yi bayan ta farko, sun jijjiga Teheran da lardunan dake arewaci da tsakiya da kuma yammacin Iran.

Shugaba Mohammed Khatami ya aike da sakon ta'aziyya, ya kuma umurci ministan harkokin cikin gida, Abdolvahed Moussavi-Lari, da shi kansa ya jagoranci kokarin da ake yi tare da hadin kan wasu kungiyoyi da hukumomi wajen tallafawa mutanen da suka tagayyara.

Girgizar kasa mafi muni a kasar Iran ta faru a wannan yankin kusan shekaru 40 da suka shige, ta kashe dubban mutane ta shafe daruruwan kauyuka daga doron kasa. Ana yawan yin girgizar kasa a Iran, inda a duk fadin kasar ake da manyan-manyan ramukan dake tsakanin allon doron kasa, mai kuma haddasa motsi ko girgizar kasa.

XS
SM
MD
LG