An rufe rumfunan zabe a kasar Kwango-Brazzaville, bayan da masu jefa kuri'a suka kada kuri'unsu a zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokoki.
An ce masu kada kuri'ar da suka fito ba su da yawa a zaben na jiya lahadi, wanda aka gudanar mako guda a bayan da 'yan tawaye suka kai wani harin da ya sa dubban mutane a Brazzaville, babban birnin kasar, suka ranta cikin na kare.
Har yanzu akwai kujeru 86 da ba a cike ba a wannan majalisar dokoki mai kujeru 137. Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ambaci jami'an hukumar zabe suna fadin cewa za a shafe akalla kwanaki biyu kafin a samu sakamakon zaben na ranar lahadi.
Shugaba Denis Sassou-Nguesso, yana kokarin jaddada ikonsa kan mulki a wannan babban zabe, wanda shine na farko tun lokacin da ya kwaci mulkin kasar lokacin yakin basasa a shekarar 1997. Jam'iyyarsa ta lashe 29 daga cikin kujeru 51 da aka yi takararsu a zagayen farko na zaben, inda aka yi ta zargin tabka magudi.