Sojoji masu biyayya ga shugaba Marc Ravalomanana a kasar Madagascar, sun ce suna shirin kai farmakin karshe na fatattakar sojoji masu biyayya ga tsohon shugaba Didier Ratsiraka.
Majiyoyin soja sun ce dakarun suna shirin kai farmaki a wani yankin dake kusa da Antsiranana, babban birnin lardin arewacin kasar, kuma daya daga cikin tungayen da suka rage a hannun magoya bayan Ratsiraka.
Mutanen biyu sun shafe watanni shida suna gwagwarmayar neman ikon mulkin kasar a bayan zaben shugaban kasa na watan Disamba da ake gardama kansa. Kowane dayansu yana ikirarin cewa shine shugaban kasar na halal.
Amurka ta ce ta amince da Mr. Ravalomanana a zaman shugaban kasa, kuma zata yi hulda da shi domin gaggauta kawo karshen rikicin siyasar kasar.