Bani Isra'ila 'yan share-ka-zauna sun tashi daga wasu unguwanni guda 11 wadanda aka kafa a yankin Yammacin kogin Jordan ba bisa ka'ida ba.
Cikin lumana, jiya lahadi majalisar Yahudawa mazauna wannan wuri, mai suna majalisar Yesha, ta yi watsi da wadannan unguwanni, domin yin biyayya ga umarnin da Ministan tsaron Isra'ilar, Binyamin Ben-Eliezer, ya ba ta.
An rushe gine-ginen akalla biyu daga cikin unguwannin 11, kuma Mr. Ben Eliezer ya ce bada dadewa ba, za a kassara sauran.
Ta daya gefe kuma, sojojin Isra'ila sun kashe wani mutum wanda aka bayyana da cewa, yana daya daga cikin manyan masu kera bama-bamai a kungiyar Hamas, ta Falasdinawa mayakan sa-kai.
Dakarun Isra'ila, sun ce askarawan wata runduna ta musamman, suka bindige Muhamed Taher jiya a birnin Nablus, Yammacin kogin Jordan. Isra'ila ta ce, Malam Taher ne ya kitsa wasu hare-haren kunar bakin wake da suka yi sanadiyyar mutuwar wasu 'yan Isra'ilar su fiye da dari daya.