Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Sun Yi Bukin 'Yancin Kai Na Farko Tun Bayan Hare-Haren 11 Ga Satumba - 2002-07-05


Amurkawa sun yi bukin ranar samun 'yancin kai na farko tun bayan hare-haren ta'addanci na 11 ga watan Satumba, cikin yanayi na nuna kishin kasar da aka jima ba a gani ba, kuma cikin tsauraran matakan tsaro a dukkan manyan birane da wuraren tarihi na kasa.

Dubban jama'ar da suka taru a nan birnin Washington domin kallon wasannin wuta da na mawaka na ranar 4 ga watan yuli, sai da suka bi ta cikin cibiyoyin da jami'an tsaro suka kakkafa a babban filin tarurruka da shakatawa na kasa a bayan ginin majalisar dokoki.

Mutane fiye da dubu 200 suka halarci bukukuwan na Washington.

A akasarin sassan birnin New York, an haramtawa jiragen sama yin shawagi na wani lokaci. Dubban mutane sun kalli wasannin wuta suka kuma karrama mutanen da suka mutu da gwarzayen da suka yi kokarin ceto jama'a a hare-haren ta'addancin.

A dandalin 'yanci na birnin Philadelphia, inda aka ayyana kafa Amurka, an gudanar da al'adar da aka saba kowace shekara ta kada gwarjen 'yanci. A lokacin da yake magana a kofar dakin taron da aka gina a cikin karni na 18, inda kuma aka ayyana 'yancin Amurka daga Ingila a shekarar 1776, sakataren harkokin waje Colin Powell yayi kira ga dukkan Amurkawa da su yi aiki da akidarsu ta 'yanci ta hanyar takalar talauci, da kiyayya da kuma bambanci.

Shugaba Bush ya kaddamar da nasa bukukuwan ranar 4 ga watan Yuli ta halartar bukuwan da aka yi a wani dan karamin gari mai suna Ripley a Jihar West Virginia. A cikin jawabinsa na ranar 'yanci, Shugaba Bush ya ce fiye da kowane lokaci a baya, kan Amurka ya hadu wuri guda a kudurin kare Amurkawa tare da murkushe ta'addanci.

XS
SM
MD
LG