Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maroko Da Spain Suna Kokarin Sassauto Da Rikici Kan WAni Tsibiri - 2002-07-14


Da alamun Maroko da Spain suna kokarin rage tankiyar da suke yi kan mallakin wani dan karamin tsibiri dake dab da gabar Afirka ta Arewa.

Tankiya tayi zafi ainun ranar asabar, a lokacin da Spain ta tura jiragen ruwan yaki uku zuwa yankin, kwanaki biyu a bayan da Maroko ta tura sojoji kwaya 12 kan wannan tsibirin da Maroko take kira Leila, ita kuma Spain take kira Perejil.

Amma kuma ministar harkokin wajen kasar Spain, Ana Palacio, ta ce ba za a iya bayyana matakin da kasar Maroko ta dauka a zaman harin mamaya ba, kuma Spain tana so ne kawai a koma ga zama kamar yadda aka saba yi a da, watau ba tare da sojojin maroko kan tsibirin ba.

Kafin wannan karon dai, babu wani mahalukin dake zaune a kan wannan tsibirin, wanda fallen dutse ne, wanda kuma dukkan kasashen biyu suke ikirarin cewa nasu ne.

A halin da ake ciki, kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ambaci Firayim Ministan Maroko, Abderrahmane Youssoufi yana alkawarin kaucewa kara rura wutar wannan rikici.

Shi dai wannan tsibiri tazarar mita 200 yake da ita daga bakin gabar kasar Maroko.

XS
SM
MD
LG