Manyan masu adawa na kasar Iraqi sun kafa majalisar yaki mai wakilai 15 wadda zata kula da kokarin hambarar da shugaba Saddam Hussein daga kan mulki.
Tsoffin hafsoshin sojan Iraqi da wasu masu adawar ne suka kafa wannan majalisa a taron kwanki ukun da suka kammala jiya lahadi a London.
Wannan majalisa tana karkashin tsohon Manjo-Janar Tawfiq al-Yassiri, wanda ya ki bayyana sunayen sauran wakilan majalisar. An ce har yanzu wasunsu suna zaune cikin Iraqi.
Bijirarrun na Iraqi sun ce daya daga cikin muhimman abubuwan da suka sanya a gaba shine na janyo hankalin hafsoshin sojan Iraqi da su bijire.
Amurka ta bayyana taron na London a zaman matakin ci gaba. Shugaba Bush dai ya ce Amurka zata yi amfani da duk wata hanyar da zata iya wajen hambarar da shugaba saddam, wanda take zargi da goyon bayan ta'addanci tare da kokarin neman mallakar makaman kare dangi.