Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Bukaci Isra'ila Da Ta Janye Daga Yankunan Falasdinawa - 2002-08-06


Babban zauren shawarwarin MDD ya bukaci Isra'ila da ta janye sojojinta cikin sauri daga yankunan Falasdinawa.

Majalisar ta zartas da wani kudurin da ya bukaci sojojin Isra'ila da su janye cikin gaggawa zuwa wuraren dake hannunsu shekaru biyu ad suka shige, kafin barkewar tashin hankali na baya-bayan nan.

Har ila yau, kudurin yayi tur da kai hare-hare kan fararen hula da dukkan bangarorin biyu suke yi, ya kuma bayyana tsananin damuwa kan irin ukubar da al'ummar Falasdinawa suke fuskanta.

Wakilai 114 suka amince da wannan kudurin da ba tilas ne a yi aiki da shi ba, wakilai hudu kacal suka ce ba su yarda ba, yayin da kasashe 11 suka kauracewa jefa kuri'a. An jefa kuri'ar a bayan doguwar muhawara, inda kasashe daya bayan daya daga Asiya da Afirka da kuma yankin Gabas ta Tsakiya suka ringa yin tur da mamayar da Isra'ila take yi wa yankunan Falasdinawa.

Isra'ila da Amurka suna cikin kasashe hudun da suka ki yarda da wannan kudurin hadin guiwa, wanda wakilan Falasdinawa da na Kasashen Tarayyar Turai suka zana.

XS
SM
MD
LG