Wata kungiyar kare lafiyar namun daji tayi kashedin cewa miliyoyin mutane da dabbobi a nahiyar Afirka suna cikin hadari sosai idan har duniya ta ci gaba da kara yin dumi kamar yadda take yi a yanzu.
Asusun Kare Namun Daji na Duniya yayi kira ga Amurka da sauran kasashen duniya dake shirin yin taron koli kan alkinta muhallin duniya cikin mako mai zuwa a kasar Afirka ta Kudu, da su rungumi yin aiki da makamashin da ba ya fitar da guba, maimakon irin man da ake yin amfani da shi a yanzu. Makasudin haka shine rage fitar da guba mai lalata muhalli.
Cikin wani rahoto kan canjin yanayi a nahiyar Afirka, Asusun na kare namun daji ya ce Afirka tana iya fuskantar mummunar matsalar karancin abinci da ruwan sha.
Asusun ya ce tuni har dumin da duniya ke kara yi ya lalata fiye da rabin fadamun dake gabar tekun wasu yankunan Afirka.