Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraqi Tana Neman Tallafin China A Kan Amurka - 2002-08-27


Ministan harkokin wajen Iraqi, Naji Sabri, ya roki China da ta taimaka musu wajen takalar barazanar da Amurka take yi kan gwamnatin shugaba Saddam Hussein.

A yau talata jami'in na Iraqi ya isa birnin Beijing.

Kafin su fara tattaunawa a asirce, ministan harkokin wajen China, Tang Jiaxuan, ya ce wannan ziyara ta Malam Sabri tana da muhimmanci na musamman a saboda abinda Mr. Tang ya kira manyan sauye-sauyen da aka samu a Iraqi cikin 'yan watannin da suka shige. Bai fayyace abinda yake nufi ba.

Masu fashin baki sun ce Iraqi ta kosa da ta samu goyon bayan china wajen rage irin barazanar da Amurka ke yi wa Iraqin. A zaman daya daga cikin wakilai amsu kujerun dindindin a Kwamitin Sulhun MDD, China ta sha yin kira ga Iraqi da ta kyale sufetocin makamai su koma kasar, a zaman matakin farko na kai ga dage takunkumin da aka sanyawa Bagadaza a bayan yakin Gulf na 1991.

A wani labarin kuma, shugaba Hosni Mubarak na Misra, ya ce fitina zata barke a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya, sannan fararen hula masu yawa zasu rasa rayukansu idan har Amurka ta aiwatar da barazanar kai farmaki kan Iraqi.

Shugaba Mubarak ya shaidawa gungun dalibai a birnin al-Askandariyya (Alexandria) cewar babu wata kasar Larabawan da zata bari a yi amfani ad sansanoninta wajen kai hari a kan Iraqi a daidai lokacin da Isra'ila take karkashe Falasdinawa. Ya ce Amurka ta san halin da ake ciki.

XS
SM
MD
LG