Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Tace Ba Zata Iya Ci Gaba Da Biyan Basussukan Dake Kanta Ba - 2002-08-28


Gwamnatin Nijeriya ta ce ba zata iya biyan basussukan kasashen wajen da ya kamata ta biya cikin wannan shekara ba.

A yau laraba, jami'an babban bankin Nijeriya da na ma'aikatar yada labarai suka sake nanata gargadin cewa kasar zata iya biyan rabin basussukan da ya kamata ta biya a wannan shekara ne kawai.

Suka ce daga cikin dala miliyan dubu 3 da 300 da ya kamata Nijeriya ta biya a wannan shekara, abinda gwamnati zata iya biya ba zai shige dala miliyan dubu 1 da 500 ba.

A yau laraba ministan yada labarai, Jerry Gana, ya musanta rahotannin kafofin labarai da suka ambaci gwamnan babban bankin kasar na cewa Nijeriya zata dakatar da biyan basussukan kasashen waje. Jami'an Nijeriya suka ce kasar tana da aniyar biyan wannan bashi baki dayansa.

A jiya talata, gwamnan babban bankin Nijeriya, Joseph sanusi, ya ce faduwar farashin mai ta sa zai yi wuya Nijeriya ta iya cikata alkawuranta na kudi.

Nijeriya, mai arzikin man fetur, tana daya daga cikin kasashen da bashi yayi musu kanta a duniya. Ana binta bashin kudi fiye da dala miliyan dubu 32, akasari daga gungun masu bada rance na gwamnatocin kasashen waje da ake kira "Paris Club."

XS
SM
MD
LG