Kafofin labarai sun bada rahoton cewa bam ya ragargaza hedkwatar wanbi gidan rediyo mai zaman kansa a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe.
Wani mai gadi guda daya ne kawai yake ciki a lokacin da bam din ya tashi, kuma an ce bai ji rauni ba.
Wannan gidan rediyon da ake kira "Muryar Jama'a", yana samowa da tsara labaransa a cikin kasar ta Zimbabwe, to amma kuma yana watso su ta mitoci masu cin dogon zango daga kasar Netherlands, domin kaucewa dokokin watsa labarai masu tsauri na kasar Zimbabwe.
Ba a san ko wanene ya dasa wannan bam ba, wanda ya yaye rufin ginin, ya kuma yi kaca-kaca da cikinsa. Ana daukar wannan gidan rediyo a zaman mai adawa da gwamnati.