Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Ja Kunnen Amurka Game Da Yin Amfani Da Karfi A Kan Iraqi - 2002-09-02


Rasha ta ja kunnen Amurka da kada ta kai farmakin soja a kan Iraqi, tana mai cewa yin haka zai gurgunta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun Farisa da Gabas ta Tsakiya.

Har ila yau, ministan harkokin wajen Rasha, Igor Ivanov, ya ce har yanzu Rasha ba ta koda kwayar zarra ta shaidar dake nuna cewa Iraqi tana yin barazana ga tsaron Amurka ba.

Mr. Ivanov yayi magana a bayan da ya gana da ministan harkokin wajen Iraqi, Naji Sabri, wanda yayi tattaki zuwa birnin Moscow domin neman goyon baya wajen fadada adawa da shirin Amurka na kai farmaki kan Iraqi.

Jami'an Amurka sun ce Iraqi tana da makaman kare-dangi, sun kuma ce suna son a cire shugaba Saddam Hussein daga kan karagar mulki.

Mukaddashin firayim ministan Iraqi, Tariq Azeez, ya ce zai gana da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, gobe talata a Afirka ta Kudu, domin tattauna wannan batu.

XS
SM
MD
LG