Tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela, yayi tur da kakkausar harshe da irin barazanar da Amurka take yi ta kai hari a kan Iraqi.
Mr. Mandela ya shaidawa 'yan jarida yau litinin cewa zai kufula sosai idan har Amurka ta kai hari kan Iraqi ba tare da iznin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ba.
Tsohon shugaban mais hekaru 84 da haihuwa, ya ce ya sha yin kokari, amma bai samu nasarar yin magana da shugaba Bush ta wayar tarho ba. Ya dai samu yin magana da mahaifin shugaban, tsohon shugaba Bush babba, da sakataren harkokin waje Colin Powell.
Har ila yau, Mr. Mandela ya shaidawa 'yan jarida a Johannesburg cewar bai kamata a kyale wata kasa a doron duniya ta zamo 'yar sandar kanta ba.
A makon da ya shige, mataimakin shugaba Dick Cheney, ya ce tilas a dauki kwararan matakai kafin Iraqi ta kera makaman nukiliya, ta kuma yi amfani da su wajen kwace rijiyoyin mai na duniya.